Kungiyar masu maganin gargajiya ta bukaci hadin kan gwamnati wajen ba su cibiyar da za su rika gudanar da binciken magungunan gargajiya da suke ba al’umma.
Magungunan gargajiya wadanda aksarinsu akan samu ne daga ganyaye, saiwa, sassake da ‘ya’yan itatuwa da kwayoyin tsirrai da furanni, bincike ya nuna cewa kashi tamanin na al’umman nahiyar Afirka na amfani da su.
A taron da ‘ya’yan kungiyar masu maganin gargajiya na illahirin jihohin arewacin Najeriya suka gudanar a cibiyar binciken magunguna da ke Jami’ar Jos, shugaban kungiyar a jihar Filato, Lershim Zuriya, ya ce abin da suke bukata shi ne gwamanati ta samar masu da cibiyar gudanar da bincike.
Wasu da suka halarci taron sun bayyana cewa, an sami ci gaba kwarai a yadda ake sarrafa maganin gargajiya.
Farfesa Muhammad Ibrahim Jawa ya ce kamata ya yi hukumomi su maida hankali wajen horar da masu maganin gargajiya, kamar yadda ake yi a kasashen da su ka ci gaba.
Saurari cikakken rahoton wakiliyarmu Zainab Babaji daga Jos:
Your browser doesn’t support HTML5