Kamfanonin Kasashen Ketare Za Su Kare Kan Su Kan Kin Biyan Haraji Na Sama Da $25B

Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya Femi Gbajabiamila

Kwamitin jin Korafin Jama'a na Majalisar Waklilan Najeriya ya sake gayyatar mai kwarmato Dr. George Uboh kan bahasi na zambar kudin shiga sama da dala biliyan 25 daga kamfanonin man kasashen ketare.

Wadanda za su kare kan su a zauren binciken a ranar Alhami 25 ga watan Fabrairu, sun hada da bankin Standard Chartered da Babban Bankin Najeriya CBN.

Sauran wadanda za su bayyana a gaban kwamitin sun hada har da bankin Stanbic IBTC da kamfanin wayar salula na MTN na mutan Afirka ta Kudu.

George Uboh ya nuna farin ciki cewa shugaban hukumar tara kudin shiga Muhammad Nami, a watan jiya ya tabbatar da zargin sabawa doka wajen biyan harajin na kamfanonin na ketare musamman na man fetur.

Uboh duk da haka ya bukaci Nami da ya binciki jami'an sa da ka iya zama da hannu a wajen aikata wannan laifi ta hanyar wallafa bayanai da ke rage yawan kudin da kamfanonin ke samu da aringizon kudaden da su ke kashewa wajen aikin da su ke gudanarwa.

Sakataren mai kwarmaton, Injiniya Magaji Muhammad Yaya, ya ce takardun sun nuna matukar za a gano wadannan makudan kudi, to Najeriya ba ta bukatar nemo bashin kasashen ketare wajen gudanar da manyan ayyuka ko daukar nauyin kudurorin kasafin kudi.

A zaman da kwamitin ya yi a watan Disambar bara, yawancin kamfanonin da a ke zargin sun bayyana, inda a wannan karo za'a ba su damar kare kan su.

Masu kwarmato sun rage karsashi a Najeriya don rashin samun ladar kashi 5 cikin 100 na yawan kudin da su ka bankado kamar yadda aka shardanta, kazalika hakan na jawo barazana ga rasa aikin su ko ma rayuwar su.