A kokarin da hukumar kwastam ta Najeriya ke yi na kara samun kudaden shiga ga gwamnatin Najeriya, sabanin dogaro da man fetur da gwamnatin kasar ke yi, Rundunar kwastam ta daya mai kula da jihohin Legas da Ogun ta tara kudaden shiga a watanni hudu da suka gabata na Naira biliyan 5 da miliyan 1.
Kwanturolan rundunar hukumar Kwastam ta daya, Alhaji Muhammed Ali ya fada wa manema labarai a jihar Legas cewa, kudin an same su ne daga haramtattun kayayyakin da gwamnatin kasar ta hana shigowa da su cikin kasar, kayayyakin sun hada da manyan motoci na alfarma guda 34, buhuhunan shinkafa kusan dubu 40, sai kaji ‘yan kasar waje na kankara da man girki, da kunshin tabar wiwi 3,792 da kuma katan katan na kwayoyin tramol 710.
Kwanturola Muhammed ya kara da cewa hukumar ba za ta gaji ba wajen kama haramtattun kaya ko kayan da aka yi kauron biya masu haraji, kama daga tashoshin jiragen ruwa zuwa kan iyakokin Najeriya da sauran kasashen makwabta..
Saurari cikakken rahoton Babangida Jibril:
Your browser doesn’t support HTML5