Mataimakin kwantirola, Bayero Tanko Mohammed, ya ce hukumar ta kama motar tirela dauke da shinkafa buhu 600, sai kuma wasu kanana motaci uku dake dauke da buhunan shinkafa 150. Da kuma wata mota dauke da Man girki da ta tayoyin mota.
Baki daya motocin an kama sune cikin dare a sassa daban-daban na jihohin Oyo da Osun, biyo bayan samun wasu bayanan sirri da hukumar ta yi, a cewar Bayero Tanko.
Kamar yadda hukumar kwastam ta saba a duk lokacin da sukayi babban kamu, zata gurfanar da mutanen da aka kama gaban kotu domin a tuhumesu da taka dokar ‘kasa na shigar da kaya ba tare da bin hanyoyin da suka kamata ba.
Yin fasa kwaurin kayan abinci da sauran kayayyakin amfani na yau da kullum ya zama ruwan dare a Najeriya, sai dai hukumoni na gargadin al’umma dangane da yin amfani da su, domin rashin sanin ingancin musamman ma kayan abinci.
Domin karin bayani ga Hassan Umaru Tambuwal.
Your browser doesn’t support HTML5