Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce zata ‘daukaka ‘kara domin tabbatar da cewa an yi shiri na gaske, wanda zai taimaka wajen fitar da gaskiya game da mutanen da aka zarga da yiwa dukiyar ‘kasa ta’annati.
A cewar kakakin fadar shugaban ‘kasar Najeriya, Mallam Garba Shehu, gwamnatin ta damu kwarai da gaske game da wannan matsala da aka samu, amma tuni mataimakin shugaban Najeriya wanda shima lauya ne ya jagoranci kwamitin manya-manyan jami’an gwamnati domin bin sawun yadda akayi da kuma matakan da suka kamata a dauka don warware matsalar.
Cikin muhimman matakan da kwamitin manyan jami’an gwamnatin suka bayar da shawara sun hada da samar da kwararru mutanen da zasu ke gabatar da ‘kara gaban kotu, haka kuma kafin ‘daukar magana zuwa kotu a gudanar da sahihin bincike.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Umar Faruk Musa.
Your browser doesn’t support HTML5