A cewar gwamnan galibin almajiran sun je jihar ne daga wasu jihohin arewa wasu kuma sun fito ne daga kasashen dake makwaftaka da jihar ko Najeriya.
Malam Ishak Zeru dake zama naibin limamin Masallacin Juma'a na Murtala a Kano yana da almajirai dake karatun allo a gidansa. Yana mai cewa sau tari sai a kwaso yara a ajiyewa malam ba tare da wani taimako ba. Wasu ma sun fito da yaransu ne daga wasu kasashe kafin a farga sai su gudu su barsu, ke nan a bar malamin da yaran.
Yace a duba duk wanda yake alamajiri nagari ba za'a ganshi a tituna ba ranar Asabar, Lahadi zuwa Litinin. Yace idan ana son tsarin ya tafi sosai 'yan'yan kuma su zama managarta, suga kimar karatu da kimar malamansu sai an koma tsari iri na wasu kasashe. Dole iyaye su dauki wasu nauyin abubuwan da zasu dinga yi kullum domin 'ya'yansu.
Dr Muhammad Hadi Musa masanin ilimin zamantakewar al'umma da lamuran iyali ne, ya kira gwamnatocin arewa su fito da tsarin magance matsalar gabanin su hana al'umma sakewa a shekaru masu zuwa.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani.
Facebook Forum