Tun lokacin da aka gano mutum na farko dauke da cutar a Najeriya a shekarar 1986, ba za a iya ce an samu gagarumar nasarar yaki da cutar ba.
Victor Omosehin, Shugaban kungiyar masu dauke da cutar HIV ta Najeriya wato NEPHWAN, shi ya jagoranci taron juyayin wadanda cutar ta hallaka inda ya bayyana yadda cutar ke ci gaba da yaduwa duk da kamfen na yaki da ita da ake yi inda Najeriya ke bayan Afirka Ta Kudu a yawan mutane masu fama da cutar.
Dogaro da tallafi daga ketare ke ta'azzara lamuran, wanda ya ke ganin sai duk kungiyoyi da daidaikun mutane sun shiga kamfen din.
Ya ce, da a ce an mayar da hankali sosai wajen yakar cutar kamar yadda aka aka yaki cutar Ebola, da tuni an cimma gagarumar nasara.
Omoshehin yaci gaba da cewa,abun damuwa shine yadda cutar ke yaduwa a tsakanin 'yan luwadi da basu fitowa fili su nemi magani, don tsoron hukuncin daurin shekaru 14.
Duk da haka, Hukumar yaki da cutar a Najeriya NACA, ta ce wannan sam ba dalili bane, don kowa na da hurumin samun maganin. Hakazalika, akwai yaduwar cutar a yankunan karkara saboda rashin wayewa ta wajen amfani da kariya a wajen hulda da mata masu zaman kansu, ko mummunar dabi'ar afkawa yara ko manya da miyagun mutane ke yi da fyade - lamarin da ke dada karuwa a kullum, kamar yadda hukumar ta lura.
Hukumomin Najeriya na bayyana nasarar rage yaduwar cutar ta hanyar wayar da kan jama'a da kuma bude cibiyoyin gwajin jini kyauta domin gano matsayin mutane dangane da cutar.
"Ana dubawa dangane da cutar don a tabbatar ko mutane suna da shi ko ba su da shi, idan yana da shi sai a tura shi wajen bada magani." inji Dakta Rilwan Muhammad, Babban sakataren hukumar lafiya matakin farko a Abuja.
Ya ce akwai sirri don ba a fallasa mutumin da aka gano yana dauke da cutar. Sannan suna kokarin fadakar da mata masu bin maza da su yi amfani da roba domin gujewa cutar.
Wani kalubale shine yadda tashe-tashen hankula sakamakon ayyukan ta'addanci ke jefa mutane musamman mata a sansanonin 'yan gudun hijira cikin barazanar kamuwa da cutar.
Wakiliyar kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, Michelle Simon, ta bayyana sakamakon zagayawa sansonin 'yan gudun hijira a Jihar Borno da sauran yankin tafkin Chadi, inda ta ce matan da suka rasa mazajen su ko iyayen su na fuskantar barazanar fyade da cin zarafi.
Ta ce hakan yasa Amurka ta bada gudunmuwar dala miliyan 301 domin taimakawa masu dauke da cutar da basu kwarin gwiwar cewa kamuwa da cutar ba ita ce karshen rayuwa ba.
Saurari rohoton
Your browser doesn’t support HTML5