Najeriya Ba Ta Ci Bashin Da Ya Fi Karfinta Ba - Hon. Hafizu Kawu

Hon. Hafizu Kawu

Hon. Hafizu Kawu

Wakilai daga sassan duniya, sun hallara a Washington babban birnin Amurka domin halartar taron asusun ba da lamuni na duniya wato (IMF) na shekara shekara a birnin Washignton DC na Amurka.

Taron zai duba yadda zai taimakawa kasashe masu tasowa wajen bunkasa tattalin arzikinsu, inda a wannan karon wasu ‘yan Majalisar Tarayya da kuma ma’aikata daga babban bankin Najeriya suka samu goron gayyata.

A wata hira ta musamman da yayi da Muryar Amurka, mataimakin shugaban kwamiti mai lura da harkokin bankuna da kudade na Majalisar wakilan Najeriya Hon. Hafizu Kawu, mai wakiltar karamar hukumar Tarauni a jihar Kano, ya ce akwai damarmaki na musamman a wajen wannan taron da suka gani wanda idan sun koma gida za su sanar da gwamanti shawarwari domin ta duba don inganta tattalin arzikinta.

Wani batu da jama'a a kasashe masu tasowa ke yi shi ne bankin na IMF na juya kasashensu musamman wajen karbar basussuka, sai dai Kawu ya ce ba haka lamarin yake ba.

“Najeriya ba ta ci bashin da ya fi karfinta ba, saboda Allah ya albarkace ta da yawan al’umma da ma’adinai da dai sauransu, yawancin wadanan kudade idan an karbo su ana sa su ne a harkokin ilimi, noma, layin dogo da dai sauransu,” a cewar Hon. Hafizu Kawu.

Ya kuma kara da cewa ba zai yiwu ba dole ne a ciyo bashi saboda yadda tattalin arzikin duniya ya shiga wani yanayi, wanda darajar danyan mai ya fadi wanda da shi Najeriya ta dogara.

Amma a cewar shi, zuwan gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari tana ta kokarin ta farfado da tattalin arzikin kasar, kamar hako ma’adinai da bunkasa harkar noma da dai sauransu.

Saurari cikakkiyar hirar da Ibrahim Ka-Almasih Garba da dan Majalisa Tarayya mai wakiltar karamar hukumar Tarauni, Hon. Hafizu Kawu.

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya Ba Ta Ci Bashin Da Ya Fi Karfinta Ba - Hon. Hafizu Kawu