Najeriya: An Kama Wasu Mutane Da Ake Zargi Da Sayar Da 'Biskit' Mai Hade Da Wiwi A Yanar Gizo

Wasu daga cikin kayayyakin da aka kama a hannun masu tallan wiwi (Twitter/NDLEA)

“Wadanda ake zargin sun hada da, Queen Nvene, Collins Ozoemena, Samson Peter, Chika Nvene da kuma Habila Musa.” In ji hukumar ta NDLEA.

An Kama Wasu Mutane Da Ake Zargi Da Sayar Da Kayan Kwalama Hade Da Tabar Wiwi a Shafukan Yanar Gizo

Hukumar NDLEA da ke yaki da masu fatauci da shan miyagun kwayoyi a Najeriya, ta ce ta yi nasarar cafke wasu mutane da take zargi da sayar da kayan kwalama hade da tabar wiwi a shafukan intanet.

NDLEA ta sanar da wannan kamen ne a wata sanarwa da ta wallafa shafinta na Twitter a ranar Lahadi.

An kama mutanen ne a Abuja, babban birnin Najeriya.

“A karshen makon nan, NDLEA ta cafke wani gungun masu fataucin nau’ukan biskit da kyat da aka hada da tabar wiwi da wasu kayayyakin maye ta hanyar yanar gizo a Abuja.” Sanarwar wacce ke dauke da sa hannun darektan yada labaran hukumar Femi Babafemi ta ce.

Hukumar ta ce ta gudanar da samamen ne a tsakanin ranakun Juma’a 7 zuwa Asabar 8 ga watan Mayu.

“Wadanda ake zargin sun hada da, Queen Nvene, Collins Ozoemena, Samson Peter, Chika Nvene da kuma Habila Musa.” Sanarwar ta ce.

A cewar NDLEA, mutanen sun kware wajen hada kayayyakin kwalama da ke dauke da kayan sa maye wadanda suke sayarwa a shafukan Twitter da Instagram.

Daga cikin sauran kayayyakin da aka kama a hannun gungun mutanen a cewar NDLEA, akwai babura guda biyu na kai oda, wayar salula 10 da ake kira don yin oda da kuma na’ura mai kwakwalwa tafi da gidan (laptop) da ake amfani da su wajen tallata kayan mayen a shafukan sada zumunta.