Najeriya Tace Bude Madatsun Ruwa ya Haddasa Rasa Matsugunai

Wani jami’in Najeriya yace bude wasu madatsun ruwa da aka yi a arewacin kasar ya yi sandin rasa matsunan kimanin mutane miliyan biyu.

Wani jami’in Najeriya yace bude wata madatsar ruwa da aka yi a arewacin kasar ya yi sandin rasa matsugunan kimanin mutane miliyan biyu. Kakakin gwamnatin jihar Jigawa Umar Kyari ya bayyana jiya jumma’a cewa, ambaliyar ruwan ya kuma lalata dubban gonaki. Bisa ga cewar jami’in, ambaliyar ta auku ne sakamakon bude madatsun ruwa na Challawa da kuma Tiga da jihar Kano tayi da nufin magance yiwuwar ambaliya bayan ruwan da aka rika tafkawa kamar da bakin kwarya. Kakakin gwamnatin yace ana bude madatsar ruwan kowacce shekara, sai dai bana ruwan yayi barna ainun, kasancewa an sami kwararar ruwan fiye da kima da ya sha karfin mazauna yankin. Jami’ai sun ce suna ci gaba da tsugunar da wadanda suka rasa matsugunansu a makarantu da kuma sauran gine ginen gwamnati.