A cikin hirarshi da Sashen Hausa, Mr. Dimas wanda yake da zama a Amurka ya bayyana cewa, soke zaben shugaban kasa da kotun kolin kasar Kenya tayi , da kuma bada umarnin sake sabon zabe wani lamari ne da ya kamata a yi nazari a kai kasancewa wannan ya zama wani abinda ba a saba gani ba a kasashen Afrika.
BIsa ga cewarshi, soke zaben babbar nasara ce ga starin demokaradiya, kasancewa ya nuna cewa, kotunan suna aiki., da ya zama abin alfahari. Ya kuma ce wannan ya zama babban darasi ga sauran kasashen nahiyar idan ana so a sami ci gaba da zaman lafiya.
Mr. Dimas ya bayyana aniyar shugaban kasar Kenyan Uhuru Kenyatta na sake fasalin kotun koli a matsayin mugun nufi da kuma koma baya, idan aka yi la’akari da irin asarar rayukan da aka yi sakamakon rashin gamsuwa da zabukan baya, ya kuma ce babbar jam’iyar hamayyar tana da hujja a kiran da tayi na neman a sauke jami’an hukumar zaben , a kuma sami wadansu dabam su gudanar da sabon zabe kasancewa soke zaben manuniya ce cewa, sun tafka kurakurai, abinda zai zama da wuya duk wani zabe da zasu gudaar nan gaba ya zama da karbuwa.
Ga cikakkiyar hirarsu da Sarfilu Hashim Gumel
Your browser doesn’t support HTML5