Da ribar sana’ar da nake yi ne nake biya wa kaina wasu kananan bukatu kama daga sayen handout, ko katin waya da wasu abubuwan da ba’a rasa ba inji matashiya Maryam Yusrah Ali.
Ta ce tana sana’ar sayar da huluna na mata wadanda ake kira Mansur, inda take saro su a dinke take kuma shigarwar a makarantu da wuraren kawayenta.
Ta ce ta fara sana’ar ne domin kashe wasu kananan bukatu nata ba tare da ta nema daga wajen iyayenta ba kuma hanya ce ta rage wa iyaye dawainiya.
Ta ce sana’ar ko kadan bata shafar yanayin karatunta domin sana’ar a mafi yawan lokuta ‘yan uwanta dalibai da kawayenta ne ke sayen kayan bayan sun gansu a jikinta.
Maryam ta ce fatan ta dai sana’ar ta, ta bunkasa kuma ta ja hankalin ‘yan uwanta matasa da su daure su nemi sana’ar hannu domin wata hanya ce da zasu rage zafin gari sannan a hannu gudu kuma suna gina kansu ne dan magance zaman kashe wando.
Your browser doesn’t support HTML5