Myanmar Da Bangladesh Sun Kammala Shirin Mayar Da Musulmin Rohingya Gida

Shugabar Myanmar, Aung San Suu Kyi.

Yanzu haka kasashen Myanmar da Bangladesh sun kammala shirin ganin sun mayar da musulmin Rohingya da yaki ya tilastawa barin gidajensu don ganin an mayar dasu muhallansu.

Yanzu haka kasashen Myanmar da Bangladesh sun kammala shirin ganin sun mayar da musulmin Rohingya da yaki ya tilastawa barin gidajensu don ganin an mayar dasu muhallansu.

Jami'an diflomasiyyar kasashen biyu ne suka gana a Dhaka a yau Talata don kammala wannan shirye-shiryen da suka cimma matsaya akai a cikin watan da ya gabata.

Wannan yarjejeniyar zata sa mutane da yawansu ya kai dubu dari shida ' kabilar Rohingya da suke neman mafaka akan iyakar kasar damar komawa gidajensu na asali.

Ana sa ran za a fara kwashe wadannan mutanen zuwa garuruwansu a cikin watan Fabrairun shekarar 2018 idan Allah ya kaimu.

Myanmar ta bada tabbacin cewa zata kula da 'yan kabilar ta Rohingya a lokacin da suke komawa gidanjen nasu.