Mutuwa Ta Hada Kan Gaggan ‘Yan Siyasa Da Ba Sa Ga Maciji a Sokoto

  • Murtala Sanyinna

Gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal Lokacin Jana'izar Baraden Wamakko

Rasuwar Baraden Wamakko Alhaji Salihu Barade, ta hada kan jiga-jigan siyasar jihar Sokoto, wadanda suka dade ba sa ga maciji a tsakaninsu.

Basaraken na Wamakko wanda kani ne ga tsohom gwamnan jihar Sokoto Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko kuma daya daga cikin ‘yan majalisar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, ya rasu ne da daren Laraba, bayan ya jima yana jinya.

To sai dai abin da ya baiwa jama’a mamaki shine, yadda gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal da suka raba gari da Wamakko a siyasance, ya yi sammakon halartar jana’izar mamacin da aka gudanar a safiyar yau Alhamis a garin Wamakko, duk da zafafar siyasa a tsakaninsu, wacce ta kai ga sukan lamirin juna, har ma da zarge-zargen juna.

Gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal Lokacin Jana'izar Magatakardar Wamakko

​Babban abin da yafi jan hankalin jama’a ma shine ba zato ba tsammani, tsohon gwamna Attahiru Dalhatu Bafarawa, shi ma kwatsam ya yi tattaki har garin na Wamakko, inda ya jajanta tare da yin ta’aziyya ga Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko.

Wannan lamari dai na zuwa ne kasa da sa’o’i 48 a gudanar da zaben gwamna da za’a sake a rumfuna 135 a jihar, wato ke nan, a daidai likacin da aski ya zo gaban goshi, yakin neman zabe na kankama, yayin da kuma takaddama take kara zafafa a tsakanin wadannan jiga-jigan siyasa.

Idan za’a iya tunawa, Aliyu Wamakko ne ya yi wa Attahiru Bafarawa mataimakin gwamna, daga shekara ta 1999 zuwa 2006, sa’adda a shekarar karshe ta wa’adin mulkinsu na 2, Wamakko yayi murabus, ya kuma canja sheka zuwa jam’iyyar PDP, wacce ta tsayar da shi takarar gawamna a shekarar 2017.

Wamakko yayi nasarar kada dan takarar Bafarawa wato Muhammadu Maigari Dingyadi na jam’iyyar DPP a wancan lokacin, inda kuma da hawansa mulki, ya maka Bafarawan a kotu, bisa zargin sama da fadi da dukiyar jiha, shara’ar da aka kwashe tsawon shekaru 10 ana yi, kafin kotu ta wanke Bafarawa daga laifin, watannu 4 da suka gabata.

Gwamna Tambuwal kuma, ya gaji Wamakko ne a zaben da ya gabata na 2015, sa’adda yana kakakin majalisar wakilai ta Nijeriya, ya bar jam’iyyar sa ta PDP, ya koma APC ya hade da Wamakko, ya kuma lashe zaben gwamna a karkashin jam’iyyar, to amma a shekara ta 3 ta mulkinsa, ya sake komawa jam’iyyarsa ta PDP, inda hade da su Bafarawa, ya kuma nemi tsayawa takarar shugaban kasa bai yi nasara ba.

Ya dawo takarar gwamna a wa’adin mulki na 2, inda ya tarar shi kuma Wamakko ya tsayar da babban yaronsa Ahmad Aliyu, wanda shine mataimakin gwamnan Tambuwal kafin yayi Murabus a cikin shekara ta 3 da hawansu mulki.

Duk da yake Bafarawa kamar ya rama takwarkwara ne, domin kuwa a lokacin da mahaifinsa ya rasu, Wamakko ya niki gari ha garin Bafarawa domin yi masa ta’aziyya, to amma sam ba’a yi tsammanin zuwan Bafarawa a Wamakko ba, musamman la’akari ta yanayin da ake ciki na zafafar takaddamar siyasa a tsakanin su biyun.

To sai dai sabanin tunanin mutane da dama, sai gashi hakan ya faru, lamarin da kuma ya kasance wani babban darasi ga mabiyan bangarorin guda biyu da su ma suka fatattaki juna saboda siyasa, har suke ta yayyata lamarin da kuma bada misalin wannan haduwa a kafafen sada zumunta na yanar gizo.