Mutumin Da Ya Kashe Matarsa Ya Kuma Kafe Hotunan Kisan A Facebook

court room

Kotu ta samu Derek Medina da laifin kisa, mutumin nan da ya kashe matarsa kuma ya kafe munanan hotunan kisan kan shafin sadarwarsa na Facebook.

Masu yanke hukuncin sunyi watsi da da’awar Derek na cewa ya harbi matarsa har sau takwas domin kariyar kansa gareta, saboda barazanar rayuwarsa da ya fuskanta daga matar mai suna Jennifer Alfonso.

Ya dai fadawa jami’an ‘yan sanda cewa ya kashe matarsa cikin watan Agusta na shekara ta 2013, saboda ta yi barazanar yanka shi da wuka, kuma ta kwashe shekaru masu yawa tana muzguna masa. Sai dai a bangaren masu gabatar da kara sunce Derek yayi alkawarin kashe matarsa idan har ta barshi, ita kuma abinda take shirin yi kenan.

Mahaifiyar marigayiyar taji wani sauki alokacin da kotu ta ambaci cewa an same shi da laifin kisan, biyo bayan kwashe awanni shida ana ta muhawara kan shari’ar. Shi dai Derek bai nuna ko alamar nadama ba, har aka daukeshi daga kotun cikin mari zuwa gidan kaso.