Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abubuwa 10 Da Ya Kamata Ka Sani Kan Facebook – Kashi Na 7


Yadda Zaka Takaita Masu Ganin Abubuwan Da Ka Sanya A Kan Facebook

Don kawai kana abota da yayunka, ko kannenka, ko abokan aiki, kai ko ma iyaye da ‘ya’ya da mata ko mazaje a kan facebook, ba wai lallai ne zaka so dukkansu su rika ganin dukkan abinda kake sakawa ko kake ru butawa kan shafinka na Facebook ba. Albishir a nan, shi ne akwai hanyar da z aka iya hana duk wani wanda bna ka so ya ga wani abinda ka sanya a facebook din.

Ga misali, idan wani labari kake son rubutawa, ko dai wani abu ya faru da kai, watau abin nan da ake kira STATUS UPDATE a turance, sai ka rubuta kamar yadda ka saba rubutawa.

Amma kafin ka matsa inda aka rubuta POST ka tura shi yadda kowa zai gani, sai ka tsaya tukuna ka natsu, ka matsa inda aka rubuta FRIENDS, watau abokai, ko kuma aka ce PUBLIC, watau kowa da kowa, ko kuma aka sa FRIENDS OF FRIENDS, watau abokan abokanka na Facebook.

Daga dan shafin da zai bude maka, kana iya zaben wadanda kake son su ga abinda ka rubuta din nan. Idan ka zabi inda aka rubuta FRIENDS, dukkan abokanka na Facebook zasu ga wannan abu. Idan ka zabi FRIENDS of FRIENDS, dukkan abokanka na Facebook su ma da abokansu na Facebook din zasu iya gani.

Idan ko ka zabi PUBLIC, to duk wani wanda yake da shafin Facebook yana iya ganin wannan abu da ka rubuta. Ba wai lallai zai tura ma kowa da kowa a duniya ba ne, amma dai duk mai so na iya dubawa.

Matakin farko ke nan na takaita wadanda zasu ga abinda ka rubuta.

Amma idan akwai wani daga cikin abokanka, ko wasu daga cikin abokan naka ne b aka son su ga wannan abu da ka rubuta, to akwai hanyar da zaka oiya toshe wasu kada su gani, yayin da sauran jama’a irin mu zamu iya gani, idan ba mu din ake son toshewa a hana ba ke nan.

Haka ma idan akwai wasu mutane kalilan ne kawai kake son su gani baka son sauran ya ayyu han nas su gani, to duk hanya day ace, ga kuma yadda ake yi:

Idan ka rubuta, kafin ka matsa POST din, sai ka bude inda aka rubuta FRIENDS ko PUBLIC ko FRIENDS of FRIENDS kamar yadda muka yi bayani da farko. A kasa, zaka ga inda aka rubuta MORE, ko kuma MORE OPTIONS, sai ka matsa wannan. Idan ka matsa, sai ka zabi inda aka rubuta CUSTOM ka matsa.

A shafin da zai bude maka, sai ka zabi mutanen da kake son su gani a inda aka ce SHARE WITH. A kuma inda aka rubuta DON’T SHARE WITH, sai ka rubuta sunayen abokanka da b aka son su ga wannan abinda ka rubuta.

Idan kana amfani da Facebook APP na ANDROID koi PHONE ne, abinda zaka yi shine sai ka matsa inda aka rubuta FRIENDS a wurin da ka rubuta abinda kake son rubutawa, sai ka zabi inda aka ce FRIENDS EXCEPT, watau abokanka su gani, amma ban da, sannan sai ka rubuta sunayen wadanda b aka son su gani din a wurin.

A kashi nagaba, zamu fada muku yadda zaku hana mutane sanya abinda ba ku so a shafukanku, sai abinda kuka amince da shi kawai.

Saurari cikakken bayanin.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG