Akalla mutum 9 suka mutu sannan wasu da dama suka ji raunuka yayin da dakarun gwamnati suka yi kokarin tarwatsa masu zanga zanga da suka yi zaman dirshan a tsakiyar birnin Khartum da ke Sudan, a cewar majiyoyin likitocin Sudan da kuma kwamitin likitocin bangaren ‘yan adawa.
A yau Litinin an ji fashewar boma bomai da kuma karar harbe harben manyan bindigogi yayin da jami’an tsaron suka tunkari wurin da masu zanga zanga suke zaune a wajen shelkwatar sojojin kasar.
Kamfanin dillanci labarai na Reuters, wanda ya ruwaito labaransa daga gidan talabijin na SKY News na larabci, ya ce mai magana da yawun gwamnatin sojin wucin gadi a Sudan, ya ce samaman da aka kai, ya kaikaici wani gungun masu aikata manyan laifuka ne a kusa da inda masu zanga zangar suke.
Amma ya ce babu abin da ya sami masu zanga zangar.
Ofishin jakadancin Amurka da ke Khartum ya wallafa wani sakon Twitter cewa, “dole a dakatar da hare-haren da ake kai wa akan masu zanga zanga.”