Mutum-Mutumi Zai Fara Marabtar Baki A Kasar Italiya

Mutum mutumin kasar Italy da ake kira Robby Pepper, ya shirya tsaf domin fara aiki a otal otal dake arewacin kasar Italy.

Shi dai wannan mutum mutumi an kirkire shi ne a kasar Japan, kuma an yi amfani da wannan fasaha ne domin taimakawa ayyuka makamantan na otal da bankuna, kuma an tsara shi a kan yadda zai iya tarar baki da kuma amsa tambayoyi idan mutum na bukata.

Robby, zai iya amsa tambaya cikin harsuna uku, harshen turanci da jamusanci da kuma Italiyanci, sai dai ana kyautata zaton masu zuwa yawon bude ido na kakar bana zasu ba mutum mutumin mamaki da tambayoyi kafin ya saba da cudanya da harsuna daban daban.

Daga karshe, kwararru sun bayyana cewa salon Magana da harsuna daban daban zai taimaka wajan kara budewa Robby ido da hazaka wajan fahimtar harsunan duniya daban daban da kuma tarbar jama’a da inganta mu’amala da jama’a.

Your browser doesn’t support HTML5

Mutum Mutumi Zai Fara Marabtar Baki A Kasar Italiya