Mutum Miliyan 3.6 Suka Kamu Da COVID-19 a Amurka

Adadin wadanda suka kamu da cutar COVID-19 a Amurka ya kai miliyan 3.6 a ranar Juma’a 17 ga watan Yuli inda ya kere na sauran kasashen duniya a cewar kididdigar jami’ar Johns Hopkins, yayin da rahoton masu kamuwa da cutar a duk rana ke ci gaba da karuwa sosai, kuma a daidai lokacin da wani rahoto daga fadar Shugaban Amurka da ba a wallafa ba ya ba jihohi 18 shawarar daukar tsauraran matakan takaita harkokin yau da kullum saboda cutar.

Rahoton ya bayyana jihohin a matsayin wadanda "lamarin ya baci sosai" saboda sun samu adadadin mutum sama da 100 a cikin gungun mutum 100,000 da suka kamu da cutar a makon da ya gabata. Cikin jihohin har da Florida, South Carolina, Texas, dukkansu sun bada rahoton adadi mai yawa na wadanda suka mutu sanadiyyar cutar ranar Alhamis 16 ga watan Yuli.

Shawarwarin da rahoton ya bada sun sha bamban da matakin Shugaba Donald Trump, wanda ya sa jihohi suka bude harkokinsu na yau da kullum duk da cewa cutar na ci gaba da yaduwa.

An kai tawagar jami’an kiwon lafiya na soja jihohin Texas da California don su taimaka wajan jinyar masu coronavirus a asibitocin da suka sosai cika.