Mutum Kusan 30 Aka Kashe a Karshen Makon Nan a Amurka

Jami'an tsaro suna bincike a wurin da aka kai harin na Dayton

Wannan hari na baya-bayan nan, na zuwa ne ‘yan sa’o’i bayan wani harin kan-mai-uwa-da-wabi, da aka kai a garin El paso da ke jihar Texas, a kantin sayar da kayayyaki na Walmart, inda mutum 20 suka mutu kana wasu 26 suka jikkata.

‘Yan sanda a birnin Dayton da ke jihar Ohio a tsakiyar yammacin Amurka, sun ce wani dan bindiga ya kashe mutum tara ya kuma jikkata wasu 16.

A yau Lahadi rundunar ‘yan sandan ta bayyana kai wannan harin a shafinta na Twitter, inda ta ce “nan da nan ta tura jami’anta a lokacin da aka kai harin, kuma sun yi nasarar dakile shi ba da bata lokaci ba.”

‘Yan sandan sun ce an kashe, dan bindigar da ya kai harin, ba tare da sun ambaci sunansa ba.

Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya ruwaito mai mukamin Magajin Birnin na Dayton, Nan Whaley tana cewa, maharin ya sanya rigar sulke, ya kuma rike wasu karin harsashai wadanda zai dura idan na cikin bindigarsa sun kare.

Wannan hari na baya-bayan nan, na zuwa ne ‘yan sa’o’i bayan wani harin kan-mai-uwa-da-wabi, da aka kai a garin El paso da ke jihar Texas, a kantin sayar da kayayyaki na Walmart, inda mutum 20 suka mutu kana wasu 26 suka jikkata.

Tuni dai ‘yan sandan yankin suka ce suna binciken wannan hari a matsayin na nuna kiyayya.

Wani sako da aka wallafa a yanar gizo gabanin harin, ya nuna kalamai na kiyayya da ke korafi kan yadda “al’umar Hispaniyawa suka mamaye” jihar ta Texas.

Mutumin da ya wallafa wannan bayani, ya ce, akwai yiwuwar a kashe shi idan ya kai hari.

"Harin yana da alaka da laifin nuna kiyayya, hukumar binciken manyan laifuka ta FBI na duba lamarin da sauran hukumomin tarayya, amma a halin da ake ciki a yanzu, muna duba yiwuwar tuhumar maharin da laifin kisa.” in ji, shugaban ‘yan sandan garin na El Paso, Greg Allen.

Rahotanni sun ce ana tsare da wani matashi farar fata mai shekaru 21, wanda shi ake zargi da kai harin.