A yanzu haka dai ta tabbata Amurka ta zarta miliyan biyu a adadin masu dauke da cutar coronavirus.
A cewar kididdigar Jami’ar Johns Hopkins da ta wallafa a shafinta na yanar gizo, Amurka na da adadin mutanen da aka tabbatar suna dauke da cutar COVID -19 miliyan 2 da 464 (2,000,464) wadanda suka mutu kuma dubu 112,924, in da ta rike matsayinta na kasar da ke kan gaba da wanna cutar.
Kusan jihoji 21 ne suka samu adadi masu yawa na masu COVID 19 a wannan makon, da yansu sun fito ne daga jihohin dake yammaci da kudu maso yammacin kasar da suka hada da New Mexico, da Texas da Utah. Hakan ya faru ne sanadiyyar sassauta dokar hana fita na kwanakin nan, ciki har da ranar tunawa da ‘yan mazan jiya.
Karuwar cutar a baya bayan nan ta sanya jami’an lafiya a jihar California soke wani bukin raye raye da wake wake da nunin zane zane da aka saba yi duk shekara a watan Oktoba. Bukukuwan an saba yinsu ne a watan Afrilun kowane shekara sai aka dage yayin da bullar cutar ta fara yaduwa.
Masana ma na nuna fargabar kada zanga zangar da aka gudanar a fadin kasar, biyo bayan mutuwar ba-Amurke bakar fatar nan a Minneapolis a hannun ‘yan sanda ya dada yawan masu kamuwa da COVID -19. Hotuna sun nuna masu zanga zangar sun kasance kafada kafada duk ta cewa wasu na sanye da takunkumin rufe hanci da baki
Duk da haka, jami’an shahararren filin wasan yara na Disneyland a California sun sanar jiya Laraba za fara matakin farko na bude wurin a ranar 17 ga watan Yuli wanda zaiyi daidai da cikar bude gurin shekara 65.