Mutum Dubu 25 Kawai Za a Bari Su Shiga Kallon Wasan Super Bowl

(HADA HOTON AKA YI) Dan wasan Chiefs Patrick Mahomes, Hagu da Tom Brady na Buccaneers , Dama

Saboda annobar coronavirus, ‘yan kwallo 25,000 kacal za a bari su shiga kallon wasan kwallon kafar Amurka na karshe da ake kira Super Bowl wanda za a yi a ranar Lahadi.

Wasan wanda za a yi shi a filin wasa na Raymond James da ke birnin Tampa a jihar Florida zai karbi bakuncin kungiyoyin Chief da Buccaneers da za su kara a wannan wasa na karshe.

Mutum 65,890 filin yake ci, amma saboda ana so a dakile yiwuwar yada cutar COVID-19 ya sa hukumomi suka takaita ‘yan kallon zuwa 25,000.

Wannan shi ne karon na farko da wasan, wanda kusan daukacin Amurkawa suke kallo zai samu mafi karancin ‘yan kallo da za su shiga filin wasa don kallon wannan karawa.

Daga cikin wadannan ‘yan kallo, 7,500 ma’aikatan lafiya ne da aka musu allurar riga-kafin cutar corona.

Ana kuma sa ran za a jinjinawa ma’aikatan lafiya a wannan wasa, saboda irin namijin kokari da suke yi wajen kula da jama’a yayin wannan annoba.

Wasa mafi karancin masu kallo da aka taba gani shi ne wanda aka yi a shekarar 1967, inda ‘yan kallo 61, 946 suka shiga kallon wasa.

Wasan Super Bowl da ya fi samun ‘yan kallo, shi ne wanda mutum 103, 985 suka shiga kallo inda Steelers ta lallasa Los Angeles Rams.

Shi dai wannan wasa na zari-ruga wanda ya fi kowane wasa farin jini a Amurka, ya kasance wasa da al’umar kasar suke karramawa suka kuma mayar da shi wata hanyar nishadi ta musamman.