Mutum Biyar ‘Yan Gida Daya Sun Mutu A Enugu

Hedkwatar 'yan sandan jihar Enugu a kudu maso gabashin Najeriya

Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa, mutanen sun kwanta lafiya, amma da aka wayi gari da safe sai ba a ji duriyarsu ba, da aka duba sai aka tsinci gawarwakinsu a dakunansu.

Rundunar ‘yan sandan jihar Enugu a Najeriya, ta kaddamar da bincike kan abin da ya yi sanadin mutuwar wasu mutane biyar ‘yan gida daya.

Wata sanarwa da jami’in yada labaran rundunar DSP Daniel Nduke ya fitar ta ce, lamarin ya faru ne a ranar Asabar da misalin karfe 9:25 na safe a unguwar Obollo-Afor da ke karamar hukumar Udena a jihar ta Enugu da ke kudu maso gabashin kasar.

“Kwamishinan ‘yan sandan jihar Enugu, CP Ahmed Ammani, ya ba da umarnin a gudanar da cikakken bincike don gano abin da ya yi sanadin mutuwar farar-daya da ta samu Mrs. Chinyere Odoh.” Sanarwar ta ce.

Mrs. Odoh ta rasu ne tare da ‘ya’yanta biyu – Udochukwu Odoh mai shekaru bakwai da Chukwuemeka Odoh mai shekaru 4, sai kanenta mata biyu – Martina Ezeme da Ngozi Ezeme kamar yadda sanarwar ta DSP Nduke wacce aka wallafa a shafin Facebook din rundunar ta nuna.

Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa, mutanen sun kwanta lafiya, amma da aka wayi gari da safe sai ba a ji duriyarsu ba, da aka duba sai aka tsinci gawarwakinsu a dakunansu.

“Sai da aka fasa kofofin dakunan da suka kwana a ciki.” In ji Nduke.

Kwamishina Ammani ya kwatanta lamarin a matsayin abin takaici yana mai mika sakon taa’ziyyarsa ga iyalai da abokan mamatan.