Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

KASUWA A KAI MAKI DOLE: Hada Hadar Kasuwanci a Kasuwar ‘Yan Kifi Ta Garin Ogbete A Enugu, Yuli 17, 2022


Yayin da ake hada hadar sayen kayen masarufi a wata kasuwa a Kano
Yayin da ake hada hadar sayen kayen masarufi a wata kasuwa a Kano

Shirin kasuwa a kai maki dole na wannan makon ya leka fannin ‘yan kifi a kasuwar garin Ogbete da ke Enugu babban birnin jihar Enugu, inda wakilin Muryar Amurka Alphonsus Okoroigwe ya yi hira da ‘yan kasuwar.

WASHINGTON, DC - Kaka Madu Waziri, shi ne shugaban kasuwar ‘yan kifin garin Ogbete, ya bayyana damuwa game da tsadar kifi a yanzu da ya ce na shafar harkar kasuwancinsu.

A kasuwar dai ana saida kifi iri iri da suka hada da karfasa, tarwada, garin kifi da sauransu, amma a yanzu kifin karfasa aka fi saye saboda farashinsa na da dan sauki, duk da cewa ‘yan garin sun fi son mangala, wato tarwada kenan, a cewar Waziri. Ya kuma bukaci gwamnati ta duba lamarin don a samu sauki.

Wasu ‘yan kasuwar su ma sun koka kan yadda farashin kifin ke tashi a koda yaushe.

Yushe'u Mati, na daga cikin masu saida kifi a kasuwar, ya ce daidai gwalgwado suna samun ciniki duk da cewa farashin kifin ya yi tsada.

Shi kuma Alexander Okere cewa yayi yanayin kasuwar kifin na canzawa, wani lokacin ta yi sama wani lokacin kuma ta kwanta, musamman a lokacin damina.

Saurari shirin da Alphonsus Okoroigwe ya gabatar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:08:44 0:00
XS
SM
MD
LG