Jihar Florida da ke Amurka, ta kafa sabon tarihin zama jihar da ta fi samun adadi mafi yawa a rana guda na sabbin wadanda suka kamu da cutar COVID-19.
Sabbin alkaluman sun bayyana ne ranar Lahadi 12 ga watan Yuli inda jihar ta samu mutum 15,000 da suka kamu a rana daya, wannan adadin ya haura na duk wata jiha da aka samu a baya.
Adadin sabbin wadanda suka harbu da cutar da ya kusa da wannan shi ne na jihar California wanda ya kai 11,694 a ranar Laraba 8 ga watan Yuli.
A halin da ake ciki, jihar Florida na da kusan jimillar mutum 270,000 da aka tabbatar sun kamu da cutar sannan mutum 4,346 suka mutu.
Cikin ‘yan makonnin da suka gabata hukumomi a jihar ta Florida suka sassauta dokokin da aka saka na dakile yaduwar cutar, ciki har da bude dandalin wasannin yaran nan na Disney World, duk da shawarwarin da masana kiwon lafiya suka bayar na a guje wa cunkoson jama’a.
A ranar da adadin wadanda suka kamu da cutar a Amurka ya kai dubu 66,528 a rana guda, a karon farko an ga shugaba Donald Trump ya saka takunkumnin rufe baki da hanci a yayin wata ziyara da ya kai wata cibiyar kiwon lafiya da ke wajen birnin Washington.