Mutum 5 Sun Mutu a Sabuwar Zanga Zangar Sudan

Wata kungiyar likitoci a Sudan ta ce an kashe mutum biyar kuma wasu da dama sun jikkata a zanga zangar da aka yi, yayin da ake ci gaba da nuna adawa ga mulkin soja a Sudan.

A jiya Lahadi, dubban masu zanga-zanga sun taru a sassan kasar suna kira da a mika mulki ga gwamnatin farar hula, bayan kusan watanin uku da sojoji suka hambarar da Omar al-Bashir wanda ya yi shekara da shekaru yana mulki.

Masu zanga zangar, wadanda wasunsu ke dauke da tutar kasar, sun yi ta rera waka suna kiran da a mika mulki ga farar hula, tare da bayyana fatan majalisar gwamnatin wucin gadi ta soji da Janar Abdel-Fattah Burhan ke jagoranta za ta kife.

Zanga-zangar ta ranar Lahadi, ita ce ta farko tun bayan wani samame da jami’an tsaron kasar suka kai wanda ya tarwatsa masu zaman dirshan a Khartoum, samamen da ‘yan adawa suka ce ya yi sanadin mutuwar mutum 128.