Mutum akalla 32 ne suka mutu, baya ga wasu 190 da suka ji raunuka sanadiyyar turereniyar da ta auku a wurin jana’izar babban kwamandan sojin Iran, Qassem Soliemani, a cewar kafafen yada labaran gwamnatin Iran a yau dinnan Talata.
Dubun dubatar mutane ne suka dunguma zuwa Kerman, garinsu marigari Soliemani, don masa jana’iza da kuma ban-kwana, bayan wata hidima makamanciyar wannan da aka yi a wannan makon a Tehran, da Qom, da kuma Ahwaz.
Kafafen yada labaran na gwamnati sun ce saboda wannan turmutsitsin har sai da aka dage jana’izar.
Kisan Soliemani da Amurka ta yi makon jiya a wani harin jirgin sama ya janyo fargabar yiwuwar a fuskanci fadadden tashin hankali, yayin da Amurka da Iran ke ci gaba da barazanar daukar tsauraran matakai kan juna.
Tun da farko a yau din Talata, Jagoran Rundunar Juyin Juya Halin Iran Hossein Salami, ya yi barazana ta baya-bayan nan ta mayar da martanin soji saboda harin da Amurka ta kaddamar a wajen filin jirgin saman Iraqi da ke birnin Bagadaza.
A halin da ake ciki kuma Ministan Harkokin Wajen Iran, shi ma ya yi wani sabon gargadi ga Amurka, saboda kashe baban janar din Iran din da ta yi.
Mohammad Javad Zarif ya yi wannan barazanar ce yayin wani jawabi a wata tattaunwar da aka yi a birnin Tehran a yau dinnan Talata, wanda ya samu halartar wasu manyan ‘yan siyasa da ma’abota ilimi na yankin.
Mohammed Javad Zarif ya ce, “Labudda, Amurka za ta fuskanci takamammiyar ramuwar gayya, a lokaci da kuma wurin da hakan zai ma ta zafin gaske, saboda abin da ya kira rashin hankalin da ta nuna.”
Jana’izar ta Soleimani, wadda ta ga cincirindon jama’a a garin haihuwarsa, ta kawo karshen matakai daban daban na makokin da aka yi a sassa da dama na kasar a cikin kanakin da su ka gabata.