Mutum 15 Ke Mutuwa a Titunan Najeriya a Kullum - Rahoto

Wani hatsarin mota da ya auku

Hukumar kididdiga ta Najeriya ta wallafa wannan rahoto a shafin ta, inda yanzu ake jiran sabon rahoto da zai tabo yanayin hatsari musamman a lokacin bukukuwan da su ka wuce.

A duk wuni a Najeriya,akalla mutum 15 kan rasa ransu sakamakon hatsarin mota kan titunan kasar da aka fi danganta shi ga tukin ganganci da rashin bin dokokin hanya.

Hukumar kididdiga ta Najeriya ta wallafa wannan rahoto a shafinta, inda yanzu ake jiran sabon rahoto da zai tabo yanayin hatsari musamman a lokacin bukukuwan da su ka wuce.

Bayanan dai na nuni da cewa akan samu hatsari sakamakon tukin ganganci da kuma shan barasa kafin hawa kan titi da hakan ya shafi masu shan kwayar kara kuzari don yin jigilar fasinja ba tare da gajiya ba.

Manyan dalilan na samun hatsarin ma ba su tabo batun rashin kyan hanya, ko rashin magogin gilashi idan ana tafka ruwan sama.

Hukumar kiyaye aukuwar hatsari kan sanya jami’anta kan tituna ne da rana, inda da yamma ko da dare lokacin tituna sun rage zirga-zirga jami’an kan janye daga hanya.

Sannan kazalika akwai wata sabuwar matsala ta aukuwar hatsarin, idan an samu akasin cin karo da ‘yan fashi da hakan kan tilasta direbobi tsayawa ko su nemi banke shinge don tsira da hakan kan kare da bude wuta daga miyagun iri.

Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya daga Abuja:

Your browser doesn’t support HTML5

Mutum 15 Ke Mutuwa a Titunan Najeriya a Kullum - Rahoto