Mutum 11 Sun Mutu Bayan Fashewar Tankar Mai A Uganda

Yadda tankar mai ta kama da wuta a Uganda (AP)

Wannan mummunan yanayi ya yi kama da wani lamari makamancin wannan da ya faru a Najeriya makon da ya gabata wanda ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 140, ciki har da yara kanana.

Akalla mutum 11 ne suka mutu a ranar Talata bayan da wata motar daukar man fetur ta fashe a kusa da hanya a Uganda, a cewar ‘yan sanda.

Motar ta kife bayan wani hatsari, sannan daga bisani ta fashe a wani gari da ke kusa da Kampala, babban birnin kasar, kamar yadda kakakin 'yan sanda Patrick Onyango ya bayyana.

Wani bidiyo da wani mai kallo ya wallafa a intanet ya nuna yadda mutane ke diban man daga cikin motar kafin ta yi bindiga

Wannan mummunan yanayi kamanceceniya da wanda ya faru a Najeriya makon da ya gabata wanda ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 140, ciki har da yara kanana.

Mutanen da ke hanzarin zuwa wurin don tattara man fetur daga motocin da suka sami hatsari na fatan siyar da shi, duk da gargadin da ake yi musu su nisanci irin wadannan wuraren.

An samu irin wadannan al'amura da dama tsawon shekaru a yankin Gabashin Afirka.

Akalla mutum 62 ne suka mutu a Tanzania a shekarar 2019 yayin da suka yi kokarin zubar da mai daga wata motar da ta samu matsala.

A Kudancin Sudan, akalla mutum 183 ne suka mutu a shekarar 2015 lokacin da daruruwan mutane suka taru a kusa da wata motar daukar man fetur domin tattara man.