Mutum 1 Ya Rasu 40 Kuma Sun Jikkata Wajan Ruguguwar Shiga Kallon Kwallo

A kalla mutum daya aka hallaka kuma kimanin 40 suka ji rauni a cikin wata hayaniya wajan shiga kallon wasan kwallon kafa a filin wasan dake Madagascar.

Wannan lamarin ya faru ne kafin a fara wasan Madagascar da Senegal na neman tikitin shiga kofin kasashen Afrika, 2019

Hakan ya faru ne sakamakon Dubban masu sha'awar kallo suna kokarin shiga filin wasa ta hanya daya tilo a ranar wasan wanda aka tashi 2-2

Biyu daga cikin wadanda ke fama da raunin suna cikin mummunan yanayi a asibitin babban birnin kasar Antananarivo. Mutane da yawa sun yi ta hargitsi tun daga farkon safiya ranar wasan don sanun shiga filin wasa a Stade Municipal de Mahamasina.

Ku Duba Wannan Ma Wainar Da Ake Toyawa A Fannin Wasan Tamola A Duniya

Manema labarai sun ruwaito cewa jama'ar sunyi ta gaggawa domin shiga filin wasa sai kawai kofar ta bude.

Dan wasan Manchester United mai shekaru 23 da haihuwa, Luka Shaw ya sa ido a kulob din, yana jiran sabuwar kwangila inda ta bayyana cewa aikinsa zai ƙare a karshen kakar wasa ta bana.

Kungiyar Leicester tana shirin kara wa dan wasan bayanta Harry Maguire's, Sabuwar kwankigilar zata kawo karshen zawarcin da Manchester united, take yi wa dan wasan mai shekaru 25 da haihuwa.

Kocin Chelsea Maurizio, Sarri yana son shiga zawarcin dan kasar Italiya Alessio Romagnoli, mai shekaru 23, da Mattia Caldara, dan shekaru 24, a duniya amma ta ce sai watan Janairu.

Tsohon Kocin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Zinade Zidane ya ce kwanannan bada jimawaba zai dawo cigaba da aikinsa na horas da ‘yan wasa inda ake alakantashi da komawa kungiyar Manchester united, in har ta sallami kocinta Jose Mourinho.

Your browser doesn’t support HTML5

Mutum 1 Ya Rasu 40 Suka Jikkata Wajan Ruguguwar Shiga Kallon Kwallo