An bayyana sunayen 'yan wasan kwallon kafa guda uku wadanda za su fafata wajen neman lashe lambar yabo ta gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya bangaren Maza na 2018.
'Yan wasan suka hada da Cristiano Ronaldo, Luka Modric da Mohammed Salah wadanda suka tsallaka zuwa matakin karshe na zaben.
Sai dai kuma dan wasan gaba na Barcelona dan asalin Argentina Lionel Messi, wanda ya taba lashe kyautar na Ballon d'Or, sau biyar ba ya cikin mutune uku na karshe da za su fafata takarar ta bana.
Bayan haka kuma babu wani dan wasan kasar Faransa, wacce ta lashe kofin kwallon da aka yi a Rasha a jerin 'yan wasan.
Dan wasan kasar Portugal Ronaldo, wanda ya lashe kyautar a 2016 da kuma 2017, ya samu nasarar daukan kofin zakarun turai karo na biyar a watan Mayu, a lokacin yana wasa a kungiyar Real Madrid ta kasar spain kafin komawarsa Juventus a kan fam miliyan £99.2m.
Shi kuwa dan wasan tsakiya na Real Madrid Luka Modric, dan kasar Croatia ya samu kyautar dan wasa mafi kokari a gasar kwallon kafar duniya na 2018, bayan kasarsa Croatia ta kai matakin wasan karshe na gasar inda ta fafata da kasar Faransa, ta kuma kare a mataki na biyu.
Dan wasan gaba na kasar Masar mai taka leda a Liverpool, Mohammed Salah ya ci kwallo har guda 44, a kungiyarsa ta Liverpool inda kulob din ya kai wasan karshe na gasar zakarun turai, da aka kammala 2017/18.
Ko da yake, ya sha kashi a hannun Real Madrid, amma ya kuma taimaka wa kasarsa Masar ta samu tikitin shiga gasar cin kofin duniya na bana.
Luka Modric dai a kwananna ne ya doke Ronaldo da Salah inda ya zama gwarzon dan kwallon kafar ta nahiyar turai.
Facebook Forum