Mutanen Zamanin Jahiliyya Na Afirka Sun Riga Na Turai Mallakar Fasahar Kere-Kere

Mutanen Zamanin Jahiliyya Na Afirka Sun Riga Na Turai Mallakar Fasahar Kere-Kere

Masana kimiyya na Amurka da Faransa sun ce mutanen zamanin da a kogon nan na Blombos dake kasar Afirka ta Kudu a yanzu, sun lakanci yadda ake sassaka dutse shekaru dubu 75 da suka shige.

Wani sabon nazari da aka gudanar ya nuna cewa mutanen zamanin da a yankin kudancin Afirka sun lakanci yadda ake sarewa da sassaka duwatsu domin yin makami da kayan amfani da su kafin turawa su iya yin haka.

Wasu masana kimiyya na Amurka da Faransa sun ce mutanen zamanin da a kogon nan na Blombos dake kasar Afirka ta Kudu a yanzu, sun lakanci yadda ake fere dutse shekaru dubu 75 da suka shige. Turawa ba su koyi irin wannan fasahar ba sai shekaru dubu 20 da suka shige, watau shekaru dubu hamsin da biyar a bayan da ‘yan Afirka suka iya.

A irin wannan dabarar, ana amfani da k'ashin wata dabba wajen wasa dutse har sai ya zamo wuka ko wani makamin da ake bukata.

Wani jami’in kula da kayayyaki a Dakin Ajiye Kayan Tarihi na Jami’ar Colorado, Paola Villa, yace wannan abu da aka gano yana da matukar muhimmanci a saboda ya nuna cewa ashe mutanen zamanin da sun jima da lakantar yadda ake sassaka makami da kayan amfani.