Mutanen Taraba Sun Nuna Damuwa Ga Dokar Hana Fita

Mataimakin Gwamnan jihar Taraba Haruna Manu

An dai shafe kusan makwanni biyu da kafa dokar hana fitan tun daga maraice zuwa karfe shida na safe musamman a Jalingo fadar jihar Taraban.

Kafa wannan dokar ya biyo bayan wani rikici ne da aka samu a wata unguwa dake mashigar garin ta yankin ATC, lamarin da ya jawo asarar rayuka da kuma dukiya a makwanni biyu da suka shude.

To sai dai kuma duk da kwanciyar hankalin da aka samu ba a janye dokar ba, batun da yasa jama’a ke kokawa kasancewar lamarin na ci gaba da jawo tsaiko a harkar hada-hada a nan fadar jihar.

Mazauna fadar jihar sun bayyana damuwar su ga wannan matakin tsaro da hukuma ta dauka wanda suka yana tarnaki ga harkokin sun a yau da kullum.

Har sarakunan yankin sun fara nuna damuwar su game da tashin tashinan dake wakana a wasu sassan jihar Taraban.

Mai martaba Sarkin Muri Alhaji Abbas Tafida dake cikin manyan sarakunan jihar Taraba, yace abin takaici ne irin abubuwan dake faruwa a yanzu, dake da nasaba da batun kabilanci ko addini, batun da yace dole a yi karatun ta natsu.

Kawo yanzu gwamnatin jihar tace ta sassauta dokar hana fita a fadar jihar daga karfe tara na dare zuwa shida na safe, kamar yadda hadimin gwamnan jihar a kan harkokin yada labaru Mr Bala Danabu ya shaidawa wakilin Muryar Amurka ta waya.

Kamar yadda alkalumma ke nunawa jihar Taraba dai tayi fama da tashe tashen hankula dake da nasaba da fadan kabilanci ko addini fiye da sau bakwai a cikin yan watannin nan, batun da ke bukatar karatun ta-natsu.

Ga karin bayani a wannan rahoto da Ibrahim Abdulaziz ya aiko mana:

Your browser doesn’t support HTML5

KOKEN AL UMMAR TARABA