Rikicin Tiv da Jukun a jihohin Benue da Taraba da ke arewacin Najeriya, wanda ke sanadiyyar asarar dumbin rayuka da dukiyoyi, na damun Shugaba Najeriya Muhammadu Buhari, a cewar wata sanarwa dauke da sa hannun mai magana da yawunsa, Garba Shehu, wacce Muryar Amurka ta samu.
Sanarwar ta kara da cewa, Shugaba Buhari ya fara wata tuntuba kan yadda za a kafa wani kwamitin masu ruwa da tsaki, wanda zai yi cikakken bincike ya gano abin da ke haddasa rikice-rikice a tsakanin al’umomin Najeriya.
Amma kwamitin zai fi mayar da hankali ne kan rikicin na Tiv da Jukun da ya ki ci ya ki cinyewa a kwanakin nan, wanda ya rarraba iyalai ya kuma haifar da zaman dardar da rashin yadda tsakanin al’umomi, kamar yadda sanarwar ta nuna.
Sanarwar ta kara da cewa kwamitin, zai yi aiki ne da ofisoshin sakatarorin addinai, musamman na kungiyar kiristoci ta CAN da na majalisar kolin da ke kula da al’amuran addinin Islama da kungiyoyin ‘yan kasuwa da manoma da mafarauta.
Kwamitin har ila yau a cewar sanarwar zai hada har da jami’an kananan hukumomi da na jiha da sauran hukumomin jami’an tsaro.
“Shugaba Buhari na da yakinin cewa, banbance-banbancen al’umomi da Najeriya ke da shi, shi ne ginshikin hadin kanta da zaman lafiya da ci gabanta.”