Mutanen Garin Maroua Sun Yi Zanga-Zanga Kan Rushe Musu Gidaje

Wasu mata kan babura a garin Maroua na arewacin Kamaru

Zanga-zangar da aka yi yau ta biyo bayan rushe gidajen da hukumomin garin da na Jihar Arewa Mai Nisa a Kamaru suka yi a wata unguwar marasa karfi mai suna Paulina.

Mutane a garin Maroua dake jihar Arewa mai Nisa a Kamaru, sun fito rike da kwalaye a kan titunan garin yau talata, su na zanga-zangar rushe musu gidaje da hukumomi suka yi.

Wakilin Muryar Amurka, Awwal Garba, yace a baya, mutanen wannan gari sun fuskanci ukuba sosai daga hannun mayakan kungiyar Boko Haram daga makwabciyarsu Najeriya, wadanda suka yi ta kai hare-haren kunar-bakin-wake, da sace mutane musamman mata daga nan.

Sai ga shi kwatsam Kantoma da kuma magajin garin Maroua sun bayyana da manyan motocin katafila na rushe-rushe, suna rushe gidajen mutane.

Da yawa daga cikin mazauna wannan unguwa ta Paulina sun ce kwanakin baya an raba musu takardun cewa za a yi rusau, amma ba a bayyana musu lokacin da za a yi hakan ba. Da yawa suka ce sun sayi filaye a wannan unguwa sun gina gidajensu ne bisa ka'ida, kuma ba su san yadda zasu yi ba a yanzu.

Ga cikakken rahoton Awwal Garba daga Kamaru...

Your browser doesn’t support HTML5

Mutanen Garin Maroua Sun Yi Zanga-Zanga Kan Rusa Musu Gidaje Da Ake Yi - 3'03"