“Guguwar tana dada karfi sannan hadarin ta yana dada karuwa,” abin da Deanne Criswell, shugaban hukumar kwana kwanan tarayya FEMA ya fada ma CNN kenan, a Shirin “State of the Union”. Ba a san takaiaimai ta inda iskar zata kada.”
Ma’aikatan yankin sun bayyana fargababar cewa, yadda wutar take bazuwa na iya jefa yankunan da ke da yawan mutane cikin hadari su haifar da barazana ga wasu wurare masu mahimmanci a birnin da suka hada da gidan addana kayan tarihi na J. Paul Getty inda aka adana manyan ayyukan zanen da suka yi fice (shahara), da jami’ar Carlifornia, a Los Angeles, daya daga cikin manyan jami’o’in gwamnatin a Amurka.
Yayin aka shiga kwana na 6 da wutar take rurwa, alkaluman wadanda suka mutu ya kai 16, inda jami’ai suka damu cewa masu aikin ceto da karnuka masu gano gawa zasu iya gano Karin wasu gawarwakin a unguwanin da suka kone kurmus.
Dan majalisar Dattijan California adam Schiff ya fadawa CNN cewa, yayin da yake tuki a cikin unguwanin da wutar ta lakume “gaskiya ya tuna min da lokacin da na ziyarci inda ake yaki. Akwai unguwannin da gaba daya babu su kuma. Bamu taba ganin wani abu haka ba.”
A kiyasin farko da hukumar AccuWeather ta fitar ya bayyana barna da asarar dukiyoyi da aka yi ya tasamma tsakanin dala biliyan $135 da dala biliyan $150. Daga cikin dalilan da suka sa baranar ta yi yawa sossai shi ne mafi yawancuin gidajen da suka kone kurmus sun kasance cikin gidae mafe tsada a kasar.
Newsom yayi kira da a gudanar da bincike kan abin da yayi sanadin ci gaba da ruruwar da wutar take yi.