Mutane Uku Sun Mutu A Kogi Bayan Da Motar Dakon Mai Ta Kone Kurmus

Motar Dakon Mai Ta Kone Kurmus

Akalla mutane uku ne suka kone kurmus a daren ranar Litinin bayan da wata babbar tankar mai dauke da man fetur ta fashe da wuta a lokacin da ta samu matsalar birki a Lokoja, babban birnin jihar Kogi.

A cewar wani da lamarin ya faru a gabansa, hatsarin ya afku ne da misalin karfe 8:17 na dare, daura da cocin Living Faith Church, Felele, kan hanyar Lokoja zuwa Abuja mai yawan zirga-zirgar ababen hawa..

Motar mai da aka ce tana cike da dizal, tana gangarowa a gefen titi, lokacin da ta gamu da matsalar birki, lamarin da ya sa motar ta kutsa cikin wata babbar mota a kori kura kirar Dyna.

Kwamandan hukumar kiyaye hatsira ta tarayya, Stephen Dawulung, ya shaidawa manema labarai ranar Talata a Lokoja cewa mutane uku sun kone kurmus, yayin da aka ceto wasu biyu da hatsarin ya rutsa dasu da kunar wuta a jikin su aka kai su babban asibitin Tarayya dake Lokoja domin kula da lafiyarsu tare da ajiye gawarwakin a mutuwari.

“Hatsarin ya samo asali ne daga tukin banza da direban ya yi wanda ba zato ba tsammani motar ta kubuce masa. Motar dakon man dai ta kone gaba daya. Motar kirar Dyna da take ajiye a gefen hanya da wasu motoci biyu su ma wutar ta shafa,” in ji Dawulung.

Zirga Zirga motoci ta tsaya cak a wurin saboda girman wutar da ta tashi.

Bayan da gobarar ta lafa ne jami’an hukumar FRSC suka gudanar da aikin su na kula da ganin motoci sun ragu a wurin.