Mutane Na Ci Gaba Da Tofa Albarkacin Bakinsu Kan Harin Orlando

Gawarwaki bayan harin Orlando

Dubban jama’a ne a garuruwa daban-daban na Amurka ne suka fito a jiya Lahadi don nuna jimaminsu ta hanyar kunna kyadira, game da harin ta’addancin da ya hallaka mutane 50 da jikkata 53 a garin Orlandon jihar Florida ta nan Amurka.

Harin da wani haifaffen Amurka dan asalin Afghanistan Omar Siddiqui Mateen dan shekaru 29 da haihuwa ya kai akan wani gidan rawar ‘yan soyayya da auren jinsi da kuma ‘yan ba ruwanmu.

Matashin ya bude wuta da babbar bindiga da kuma ‘yar karama ta hannu da tsakar daren Lahadin da misalin karfe 2. Bayan kashe mutane hamsin ya kuma yiwa kimanin 53 mummunan raunin rai kwa-kwai mutu –kwa-kwai.

Sashen Hausa ya tuntubi wani 'dan Najeriya kuma mazaunin jihar Florida, Danladi Suleman, domin fahimtar matsayin 'yan luwadi da madigo da kuma hakkinsu a Amurka.

Danladi yace a dokar kasar Amurka duk masu neman jinsi daya na da 'yanci kamar kowa duk kuwa da cewar addini ya haramta.

Jama’ar da abin ya ritsa da su a wannan ta’addancin sun hada da mutanen da suka fito daga garuruwan garin na Orlando, Boston, Chicago, New York, San Francisco da kuma Washington.

Tsohuwar matar Omar mai suna Sitora Yusufiy ta bayyana cewa sun yi zaman aure na shekaru 2, sannan tana kallonsa a matsayin tababbe marar alkibla, tare da dukanta, wanda hakance ta sa zamansu tare na watannin 4 ne kacal.

Shugaban Amurka Barack Obama yayi tir da wannan harin da ya kira da kisan gillar da ke da nasaba da tsana da kuma tsangwamar Amurkawa, wanda ya bayyan cewa, hari akan wani bangaren ‘yan kasar, to hari ne ga dukkan Amurkawa.

Your browser doesn’t support HTML5

Harin Orlando - 1'02"