Mutane Kimanin Miliyan Daya da Rabi Ke Fuskantar Karancin Cimaka A Nijar

Alkaluman hukumomin Nijar sun bayyana cewa kimanin mutane miliyan daya da rabi ne ke cikin halin bukatar cimaka yayinda kuma ake bukatar tan dubu goma sha biyu na ciyawar dabbobi a halin yanzu.

Matsalar karancin abinci da ciyawa ya biyo bayan cije-cijen farin dango da karancin ruwan sama da kuma na ambaliyar da aka yi fama dasu daga wannan yankin zuwa wancan a cikin kasar.

Shugaban wata kungiya ya danganta lamarin da illoli irin na canjin yanayi. Yace kowa ya sani kasa ta gaji kuma ba'a tallafa mata ba. Canjin yanayi zahiri ne babu karya ko rudani ciki saboda wai sun gani. Yace bana a garin Walam har shekara ta kare basu iya shuka ba. Sun ga wasu gonaki da aka yi shuka amma kamar ba'a yi ba ne. Duk shekarar da ba'a yi shuka sosai ba to dabbobi ma ba zasu samu abinci ba.

Noman rani wani muhimmin hanya ne da hukumomi suka bullo da shi a kasar Nijar a karkashin tsarin "tuwazel" domin cike gibin da illolin canjin yanayi ke haddasawa ayyukan samarda cimaka.

Madam Maryama Altine ita ce shugabar "project" tace sun yi iri wajen ton dubu hudu suka watsa cikin karkara kuma suna aiki domin su karfafa matasa maza da mata su kara kaimi cikin aikin noma.

Saboda abun dake faruwa makiyaya na kaura daga wurarensu zuwa inda zasu iya samar ma dabbobinsu cimaka. Misali makiyayan yankunan Tawa da Agadez sun garzaya zuwa karkarar Abalak Linge. Wasu makiyayan ma sukan ketara zuwa kasashen waje saboda tsananin rashin ciyawa da ruwa.

Ga rahoton Sule Barma da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Mutane Kimanin Miliyan Daya da Rabi Ke Fuskantar Karancin Cimaka A Nijar - 3' 41"