Mutane da yawa suka ji ciwo

Tashin Hankali a Najeriya

Mutane Da Yawa Suka Ji Ciwo Sanadiyar Arangama Tsakanin Yan Sanda Ya Direbobi A Ekiti
Dubun dubatan mutane ne suka ji ciwo sanadiyar wata arangama da ta barke tsakanin yan sanda da direbobin motocin haya a Ado Ekiti babban birnin jihar Ekitin Najeriya. Lamarin ya samo asali ne yayin da wani dan sanda da ya shigo mota daga Akure zuwa Ado Ekiti ya ki biyan kudin mota, nera dari uku. Direban safa din kuma ya tsaya kan bakarsa.

Ana kan ja-in-injar ne dan sanda ya soma harbi da bindigarsa har ma akan motar safa din wadda ya yi mata kacakaca da harsashi. Lamarin ya kawo rudani matuka domin direbobi sun maida martani da yin anfani da adduna, da kujeru, da kulake da karfuna. Cikin gumutsun mutane da yawa suka ji ciwo. Wasu sun rufe shagunansu a gurguje kafin su yi babbar asara.

Lamarin ya jawo dakatar da zirga-zirgar ababen hawa na wani lokaci domin zargitsin da ya bazu a garin gaba daya.

Bayan Kaman kura ta lafa sai dan sandan da ya tsere ya dawo da wasu abokanan aikinsa. Da zuwansu tashar motar suka soma harbin kan mai uwa da wabi. Yayinda mutane suka gudu, kowa na ta kansa, yan sanda sun farma wasu da suka lakada ma kashi suka barsu rai a hannun Allah.

A halin da a ke ciki yanzu direbobin jihar sun sha alwashin kai ma kowane dan sanda suka gani a titunan garin hari. Sun kuma ce ba zasu saurarui kowa ba sai dai gwamnan jihar Dr. Kayode Fayemi