Mutane Da Dama Sun Mutu a Harin Sana'a

Wasu jami'an tsaro a birnin Sana'a dake Yemen

Wasu jerin hare-haren kunar bakin-wake ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama a Sana'a, babban birnin kasar Yemen.

a kasar Yemen ma, mutane da dama ne suka rasa rayukansu a yau juma’a a wasu masallatai biyu, bayan da wasu ‘yan kunar bakin-wake su biyu suka ta da wasu bama-bamai a Sana’a, babban birnin kasar.

Kamar yadda rahotanni suka nuna, harin ya auku ne a lokacin da za a yi salla da tsakiyar rana a masallatan Badr da na AL-Hashoosh, wadanda ake alakantawa da cewa mabiya darikar Shi’a ne na bangaren ‘yan Houthi da ke tawaye, suke kuma rike da yankin Sana’a.

Ya zuwa yanzu, Babu dai tsayayyan adadin mutanen da suka jikkata wadannan hare-haren, amma wasu majiyoyi na cewa mutane sama da 100 sun jikkata.

Su dai ‘yan tawayen Houthi wadanda suke marawa tsohon shugaban Yemen Ali Abdullah Saleh baya, sun yi wani ba-ta-kashi a ranar Alhamis din da ta gabata da mayakan sa-kai da ke goyon bayan shugaban kasar na yanzu, Abd-Rabbu Mansour Hadi.

Majalisar Dinkin Duniya da kasashen larabawa da ke yankin Gulf da wasu kasashen yammaci ciki har da kasar Amurka, duk sun nuna goyon bayansu ne ga Mr Hadi.