Mutane 7 Suka Mutu A Hare-Hare A Kankarar Jihar Katsina

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya

Sai dai 'yan sanda sun bayyana tababar ko 'yan Boko Haram ne ko kuma 'yan fashi ne suka kai hare-haren kan ofishin 'yan sanda da banki ba

An kashe wasu mutane 7 a yankin arewacin Najeriya a wasu hare-hare biyun da ake kyautata zaton cewa ‘yan kungiyar Boko Haram ne suka kai su. Shaidu sun ce wadanda aka kashe sun hada da ‘yan sanda biyar da fararen hula biyu wadanda ke kusa da wuraren da aka kai hare-haren.

An ce wasu da ake zaton ‘yan Boko Haram ne da dama sun kaddamar da hari kan caji ofis na ‘yan sanda dake garin Kankara a Jihar Katsina jiya litinin da la’asar. Haka kuma an kai wani harin dabam a kan wani banki dake garin na Kankara.

Sai dai kuma, an samu rahotanni kishiyoyin juna a kan ko ‘yan Boko Haram ne suka kai wadannan hare-hare, ko kuma dai wasu ‘yan fashi ne suka kai su. Wani mai magana da yawun ‘yan sanda yace ‘yan Boko Haram ba su cika nuna sha’awa kan kudi ba.

Wani wanda yayi ikirarin cewa shi wakili ne na kungiyar Boko Haram ya ce sune suka kai harin bam na makon jiya a kan hedkwatar rundunar ‘yan sandan Najeriya dake Abuja, babban birnin kasar, inda mutane akalla biyu suka mutu.

A cikin ‘yan shekarun nan an dora laifin wasu munanan hare-haren da suka yi sanadin hasarar rayuka a yankin Arewacin Najeriya a kan kungiyar Boko Haram. Akasarin wadanda ake kai ma harin ‘yan sanda ne da jami’an gwamnati.

Wakilin Sashen hausa, Sani Abdullahi Tsafe, ya tattauna da wani dan sandan da ya tsira da rai, da kuma hakimin Kankara, ya aiko mana da wannan rahoto da za a iya ji a kasa ko kuma a sama a gefen dama.

Saurari

Rahoton Sani Abdullahi Daga Kankara