Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar sojin Najeriya tana gudanar da tsaro a Maiduguri sakamakon hare haren bom da aka kai jiya Lahadi


Market in Maiduguri, Nigeria (file photo)
Market in Maiduguri, Nigeria (file photo)

Rundunar sojin Najeriya ta karbi aikin tsaro a birnin Maiduguri dake arewacin kasar bayan hare hare bom din da aka kai jiya Lahadi da ya yi sanadin mutuwar a kalla mutane 25

Rundunar sojin Najeriya ta karbi aikin tsaro a birnin Maiduguri dake arewacin kasar bayan hare hare bom din da aka kai jiya Lahadi da ya yi sanadin mutuwar a kalla mutane 25. Rundunar tsaron hadin guiwa sojin, ta karbi aikin samar da tsaro a Maiduguri bayan harin da ake kyautata zaton kungiyar nan ta Islama mai tsatstsauran ra’ayi Boko Haram ce ta kai. Wadansu mutane dake kan babur sun jefa boma bomai a wani gidan barasa dake babban birnin jihar suka kuma bude wuta kan mutanen dake kokarin ceton rayukansu. Kawo yanzu dai kungiyar Boko Haram bata dauki alhakin harin ba. Kungiyar ta dauki alhakin harin da aka kai a shelkwatar ‘yan sandan dake Abuja babban birnin kasar wannan watan da kuma wanda aka kai a wani gidan barasa dake Bauchi bayan rantsar da shugaban kasa Goodluck Jonathan da aka yi watan jiya. Kungiyar tace bata amince da shugabancin Jonathan ba, bata kuma amince da kundin tsarin mulkin Najeriya ba. Kungiyar ta bayyana cewa, tana neman a kafa shari’ar musulunci a kasar kafin ta tattauna da abinda ta bayyana a matsayin “kasar marasa imani”, yayinda kungiyar taci alwashin ci gaba da farautar tsofaffin gwamnonin arewacin kasar da tace suka sa a kai masu hari.

XS
SM
MD
LG