Adadin mutanen da su ka mutu a sanadiyar harin bam da aka kai da wasu motoci ranar Juma’a a Mogadishu babban birnin kasar Somalia ya haura zuwa 52, a cewar wasu bayanan asibitoci biyar da aka kai mutanen.
Jami’an tsaron Somalia wadanda su ka kai daukin gaggawa sunce ‘yan bindgar su hudu ne suka shiga Sahafi Otal, sannan su ka hau saman rufin ginin su ka yi ta harbin mutanen dake kasansu. Daga bisani jami’an tsaron suka sami nasarar kashe ‘yan bindigar, tare da ceto dinbin mutanen dake dakunan Otal din.
Tuni dai kungiyar al-Shebab wacce ta fi shekaru 10 tana gudanar da aiyukkan ta’addanci a Somalia, ta dauki alhakin kai harin.
Likitoci da jami’an asibitocin guda biyar din sun kula da mutanen da aka harba da wadanda bam ya tashi da su, sunce adadin wadanda suka mutu ya kai 52, wasu kuma 106 sun raunata.