Lura da yadda kasar Mauritania ke ci gaba da jan kafa wajen tabbatar da dokar haramta bauta kamar yadda ta yi alkawali a karakshin yarjejeniyar kasa da kasa da ta sakawa hannu, ya sa shugaban kasar Amurka Donald Trump yanke shawarar cire kasar ta Mauritania daga sahun wadanda ke cin moriyar shirin kasuwanci na AGOA, wanda a karkashinsa kasashen Afirka ke shigar da kayan sayarwa ba tare da biyan haraji ba.
Sakataren kungiyar yaki da bauta anan nijer Ali Bouzou yace wannan mataki da shugaban Amurka ya yi daida.
Shi ko magatakardan kungiyar ‘yan kasuwar Nijer masu shigo da kaya daga kasashen waje Chaibou Tchombiano, yana ganin ya kamata hukumomin Amurka su daina hada laifin aikata bauta da sha’anin kasuwanci.
Ankarar da gwamnatin Mauritania rashin dacewar bauta, wani abu ne da gwamnatin kasar ke kallonsa tamkar wani fito na fito da hukuma kamar yadda a yanzu haka suke tsare da wani dan majalisar dokokin dake yaki da irin wannan dabi’a, to amma kungiyar TIMIDRIA na ganin matakin na AMURKA zai iya kawo karshen wannan al’amari.
A watan januaryn 2019 ne matakin na shugaba Donald Trump ke fara aiki wanda masana harakokin kasuwanci ke cewa zai iya haifarwa ‘yan kasuwar Mauritania asarar kudaden shiga daga waje musamman wadanda ke fitar da kayayyaki samfarin wannan kasa zuwa kasuwanin duniya.
Facebook Forum