Mutane 189 Sun Mutu A Hadarin Jirgin Saman Indonesia

Akalla fasinjoji 189 da ma'aikatan jirgin sama lion air sun rasa rayukansu yayin da jirgin ya fada cikin teku mintina goma sha uku da tashin sa daka Jakarta babban birnin Indonesia.

Rahotanni daga Indonesia sun ce wani jirgin sama na kamfanin Lion dauke da fasinja 189 ciki har da ma’aikatan jirgin ya fada cikin teku mintina 13 da tashinsa daga birnin Jakarta.

Bayanai sun yi nuni da cewa ana fargabar dukkanin fasinjojin cikin jirgin sun rasu.

Wani mai magana da yawun kamfanin jiragen na Lion, Sutopo Purwo Nugroho ya wallafa hotunan tarkacen jirgin a shafinsa na Twitter wanda ya hada da fasassun wayoyin zamani, littattafai, jakunkuna da kuma wasu bangarorin jirgin wanda masu aikin kai ceto suka tattaro daga cikin teku.

Nugroho ya ce daga cikin fasinjojin akwai yaro daya da kuma jarirai biyu.

Yanzu haka dai hukumar aikin gaggawar kasar Indonesia ta aika kwararru masu ninkaya gurin don neman gangar jikin jirgin da ya fadi a arewa da tsibirin Java.

Wani jami’in cibiyar ya yi hasashen cewa da kyar za’a samu wanda ya tsira daga cikin wadanda ke cikin jirgin.