Mutane 13 Sun Mutu, 27 Suka Bace Bayan Nutsewar Wani Jirgin Ruwa A Gabar Tekun Tunisiya

Tunisia - Jirgin ruwa dauke da masu tserewa

Wani jami'in shari'ar kasar Tunisia ya sanar a ranar Alhamis cewa an gano gawarwakin 'yan ci-rani 13 'yan kasar Sudan, yayin da wasu 27 suka bace bayan wani jirgin ruwa ya nutse a ranar Laraba a gabar tekun Tunisiya bayan da ya taso daga Sfax.

WASHINGTON, D. C. - Mai shari'a Farid Ben Jha ya ce jirgin na dauke ne da mutane 42 dukkansu 'yan kasar Sudan, sannan an samu ceto mutane biyu.

Kasar Italiya da wasu ‘yan Tunisiya da suka shiga kasar ta jirgin ruwa

Tunisiya ta maye gurbin Libya a matsayin babbar hanyar da mutanen da ke gujewa talauci da tashe-tashen hankula a wasu wurare a Afirka da kuma gabas ta tsakiya ke samun ficewa daga arewacin Afirka da fatan samun ingantacciyar rayuwa idan suka isa Turai.

Kasar dai ta fuskanci yawaitar bakin haure tun shekarar da ta gabata, inda ake yawan samun bala'o'i da suka hada da kwale-kwalen da ke nutsewa a gabar tekun kasar, yayin da suke dauke da bakin haure daga yankin kudu da hamadar Saharar Afirka da fatan isa Italiya.

A shekarar 2023 jami'an tsaron gabar tekun Tunisiya sun gano gawarwakin bakin haure kusan 1,000 da suka nutse a gabar tekun kasar, in ji jami'an kasar, wadda hakan shi ne fiye da na kowacce shekara.

'Yan Tunisiya ma na cikin wadanda ke kokarin tsallakawa. Kimanin bakin haure 40 'yan Tunisiya ne suka bace a watan da ya gabata bayan da suka tashi a cikin wani jirgin ruwa zuwa Italiya.

-Reuters