Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa, NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane 12, bayan rushewar wani bene mai hawa uku a layin Butcher dake yankin Dilimi a cikin birnin Jos.
Jami’in hukumar shiyyar Arewa ta tsakiya, Nurudden Musa, yace sun zakulo gawarwakin mutane goma sha biyu, ciki harda hudu da suka jikkata suna kwance a asibiti inda ake musu jinya.
Ya kara da cewa, dama ginin ya dade, kuma ba zai iya daukar nauyin da aka daura a kan shi ba. Saboda tsananin abun da ya faru, yace bai tsammani za'a samu wasu da rai ba, idan an gama tono.
Kanin mai gidan daya rushen, Habib Lawal Nalele, yace Alhaji Kabiru Nalele da wasu ‘yayan sa da jikokin sa, da wasu ma’aikata, duk sun rasu a rushewar ginin. Ya kara da cewa amma sun yi tawakkali ga Allah.
Makwabcin mamacin, Alhaji Bala Baban Mairam, yace kamata yayi hukumomi su rika shiga unguwanni don duba ingancin gine-gine.
Ga cikakken rahoto daga wakiliyar muryar Amurka Zainab Babaji.
Your browser doesn’t support HTML5