Musulmi 'Yan Darikar Sufi Na Ci Gaba Da Shirye Shirye

Duk da tashin bam a masallacin 'yan darikar Sufi da ya hallaka daruruwan jama'a da raunata wasu da dama, mabiya darikar sun ce suna ci gaba da gudanar da shirye shirye.

Musulmai ‘yan darikar Sufi a kasar Masar, sun ce za su ci gaba da shirye-shiryen su na bikin murnar zagayowar haihuwar manzon Muhammad (SAW), duk da cewa kasar na jimamin harin da aka kai a wani masallaci da ke Sinai, wanda ya yi sandiyyar mutuwar mutane 305 tare da raunata 128.

Babu kungiyar da ta dauki alhakin harin da aka kai ranar jumma'a wanda ake zargin an kai ne domin ‘yan darikar sufi na ibada a masallacin Al Rawdan a wani kauye mai sunan hakan.

Sun ce za su yi bikin Mauludin, ranar Jumm'a mai zuwa a duk fadin kasar da kuma masallacin Al- Hussen da ke Birnin Al Qahira, wanda shi ne ya fi kowanne girma a kasar ta Masar.

Shugaban kasar Abdel Fattah El- Sisi ya ayyana kwanaki uku a matsayin ranakun makoki domin jimamin wannan hari da ya auku gab da Liman na shirin fara huduba.