Musulmai Sun Taya Kiristoci Bukin Kirsimeti A Nijar

Mabiya addinin Kirista

Al’ummar Musulmi a Jamhuriya Nijar sun marawa abokan zamansu Kiristoci baya wajen gudanar da bukukuwan Kirsimeti.

Daya daga cikin shugabannin al’ummar Musulmi da suka yi hira da Sashen Hausa ya bayyana cewa, Kiristoci suma suna tayasu bukukuwan Sallah saboda haka wajibi ne suma su mara masu baya. Ya kuma bayyana cewa, a cikin koyarwar Alkur’ani mai girma, wadanda suka fi kusa da Musulmi sune kiristoci.

A wannan shekarar an girke ‘yan sanda a cikin damara da wadansu cikin farin kaya a kewayen dukan majami'un Jamhuriya Nijar domin baiwa kiristocin kasar damar gudanar da harkokin ibada cikin kwanciyar hankali da salama.

Nijar dai na iyaka da jihar Sokoto inda a kwanakin baya gwamnan jihar Aminu Tambuwal ya tabbatar da cewa wadansu mutane da ake zaton yan ta'adda ne sun shiga wadansu yankuna da ke iyaka da jihohin Dosso da Tahoua a Nijer, abinda ya sa hukumomi daukar wadanan matakan kare majami'u.

Kiristoci a Jamhuriyar su kan ci gaba da gudanar da shagulgula bayan Kirsimeti har zuwa karshen shekara.

Saurari cikakken rahoton Haruna Mamman Bako

Your browser doesn’t support HTML5

Bukin kirsimeti a Nijar-4:30"

A Najeriya kuma, wadanda Sashen Hausa ya yi hira da su a Abuja sun bayyana cewa, muhimmin abinda ya banbanta bukukuwan Kirsimeti na bana da na shekarun baya shine, an gudanar da bukuwan cikin kwanciyar hankali, yayinda da dama suka sami tafiya zuwa garuruwansu, duk da matsi da wadansu ke fuskanta.